An samu firgici a wani Katafaren Kanti na 7-eleven dake birnin Bangkok na Thailand bayan da wani Wagegen Kadangare ya yi tsallen badake ya faɗa Kantin.
A wani Faifan bidiyo da ya karade shafukan yanar gizo, an ji mutane na ta karagi da kuma dariya bayan da Ƙadangaren ya ɗale kan matakalan Kantin.
Al’amarin ya wakana ne a wani yanki mai suna Nakhon Pathom dake wajen birnin Bangkok.
Sai dai ba tare da wata-wata ba wani Ma’aikacin Kantin ya kirawo jami’an yan sanda inda suka sanya majanyi suka janye Wagegen Kadangaren da samun irin shi sai an tona.
Yan sandan sun sanya majanyin inda suka lallaba shi zuwa wani Sunkuru