Rahotanni daga garin Magamar Jibia da ke karamar hukumar Jibia, jihar Katsina, sun ce a daren Lahadi misalin karfe 11:25 na dare wasu da ake zargin ƴanbindiga ne sun afka gidan wani mutum da ba a bayyana sunansa ba.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce bayan shigar mutanen ne mai gidan ya yi nasarar kashe uku tare da kone su kurmus, daga cikinsu, tare da taimakon mutanen gari, a yayin da wasu suka tsere da raunuka.
Wannan dai hare-haren ‘yanbindiga ba sabon abu ba ne, a wasu yankunan jihar Katsina, wanda ko a ranar Lahadin dai, sai da aka ba da rahoton cewa wasu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun afka garin Tudu na karamar hukumar Kankara, suka yi awon-gaba da mata da yara, suka harbi maigidan amma ba su tafi da shi ba.
Sai dai har yanzu rundunar ‘yansandan jihar Katsina ba ta ce uffan ba game da afkuwar lamarin