Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun, sun bayyana nasarar cafke wani mutum da ake zargin matsafi ne, wanda ya kashe wata mata mai sayar da abinci, sannan ya guntule mata hannaye da kai.

Lamarin dai ya faru a Ile-Ife, babban birnin jihar Osun, a ranar Asabar.

Kakakin ’Yan Sandan Osun, Yemisi Opalola ta yi karin haske dangane da afkuwar mummunan lamarin.

Ta ce matar da aka kashe din mai suna Iya Elekuru, matsafin ya ribbace ta ne ya ce ta kai masa abinci a cikin wani kangon gida domin ya saya.

“Ya ribbace ta ne da nufin zai sayi abincin ta. Da ta shiga ciki ne sai ya kashe ta, kuma ya datse mata hannaye biyu, sannan ya guntule kan ta.

“Bayan ya datse mata kai da hannaye biyu, sai kuma ya tsere da wadannan sassan jiki da ya cire daga gawar. Amma tuni jami’an mu sun dauko gawar sauran sassan jikin matar.

” Dan marigayiyar ya zo ya karbi gawar mahaifiyar sa, har an rufe ta a makabarta, bayan an sallaci gawar ta kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

” Sai dai kuma hasalallun matasa sun banka wa ginin da aka kashe matar wuta. Shi kuma wanda ya yi kisan, jami’an tsaro na nan su na ta kokarin ganin sun kamo shi a duk inda ya shiga ya boye.

An yi zargin cewa wani boka da ke zaune a cikin dakin da aka samu gawar matar ne ya kashe ta, ya kwashi sassan jikin ta sannan ya tsere.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *