A wani abu da alummar garin jogana dake karamar hukumar Gezawa a jihar kano ke cewa ba abin mamaki bane ga Manjo Janar Sunday Igbiniwahia kan irin abubuwan alheri da yake bijiro dasu lokaci zuwa lokaci ga alummar yankin a matakai daban daban kama daga harkokin binkasa Ilimi, samar da ayyukanyi ga matasa, tallafawa marasa karfi da bunkasa harkokin wasanni, da sauransu,
A lokacin daya rage kwanaki 3 a fara azumin shekara ta 2021 sai gashi major janar ya kawo wani kata faren aikin kula da lafiya alummar karamar hukumar Gezawa kyauta tare da basu magunguna da gilasai ga masu matsalar Idanu,
Dayake jawabi ga dunbin alummar da suka halarci taron da sanyi safiya a garin jogana Manjo Janar Sunday cewa yayi shin na bunkasa lafiyar alumma marasa gatane da nufin tallafa musu kamar yadda shugaban sojojin najeriya yayi umarnin a dingayi inda yace komai dadewa ana aikin soja wata rana zaa gama kuma a dawo cikin alumma saboda haka akwai bukatar a taimaki fararan hula a lokacin da suke da bukatar taimako basai lallai a harkokin tsaro ba, akwai bukatar yin aiki irin wannan a duk lokacin da bukatar hakan ta taso,
Manjo Janar Sunday wanda ya godewa alummar garin jogana bisa yadda yace sun rikeshi amana lokacin yana yaro ya kara dacewa ” Ni dan kune kuma a shirye nake na taimakeku kamar yadda kukayi min ina karami, ni dan jogana ne kuma inna alfahari daku nagode nagode” inji manjo janar Sunday,
A jawabinsa wakilin shugaban karamar hukumar kuma kakakin majalisar karamar hukumar cewa yayi alummar gezawa bazasu manta da alhairai da manjoh janar Sunday keyi wanda ke taba rayuwar alumma kai tsaye ba saboda haka sunan Sunday Igbiniwanhia zai cigaba da zama abin alfahari a alummar gezawa,
Kimanin mutane 4000 ne maza da mata yara da manya suka amfana da shirin da Manjo Janar din ya dauki nauyi