A karon farko sabon shugaban ‘yan sandan Nijeriya IGP Usman Baba Alkali ya yi wani jawabi mai sosa zuciya bayan ya kama aiki.
IGP Usman Baba Alkali ya yi alkawarin cewa zai sake karfafa rundunar ‘yan sandan Nijeriya a daidai lokacin da satar mutane, kisan rashin tunani, da duk wasu nau’ikan aikata laifuka ke addabar Nijeriya.
A cikin jawabin da sabon shugaban yan sandan ya yi, ya yi wa yan Nijeriya wasu alkawari guda uku wanda yace insha Allahu za su zama silar dawowar zaman lafiya a Nijeriya.
Jerin alkawarin da sabon shugaban yan sandan Nijeriya IGP Usman Baba Alkali yama yan Nijeriya.
1) ‘Yan sandan jiha
A wani rahoto da jaridar Tribune ta wallafa, shugaban ‘yan sandan ya tabbatarwa da’ yan Nijeriya cewa wa’adinsa zai ba da fifiko wajen kafa yan sandan jiha a matsayin babbar dabarar yaki da kawar da ta’addanci a cikin Nijeriya.
Da yake jawabin ya bayyana cewa zai ci gaba daga inda wanda ya gada ya tsaya.
IGP Baba ya ce za mu ci gaba da aiki da shi. Wanda ya gabace ni ya tafi muna a wani mataki na fari, mun fara shi amma ba mu yi nisa ba, saboda haka, duk hanyoyin an tsara su kuma za mu ci gaba da shi tare da hadin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki.
2. Inganta yanayin tsaro.
IGP din ya ce za a samu ci gaba abin yabawa a yanayin tsaron Nijeriya don haka, ya yi kira ga kowa da kowa da su taimaka wa ‘yan sanda yayin da suke tunkarar miyagun laifuka a karkashin jagoranci na hakika.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa zai sa fashi da makami da ta’addanci su zama tarihi a cikin Nijeriya da yardar Allah.
3. Sauyi a tsarin aiki.
IGP Baba ya bayyana cewa za a samu gagarumin sauyi a tsarin gudanar da ayyukan rundunar wajen magance rashin tsaro a fadin kasar.
A wani rahoto daga jaridar Punch, ya kaddamar da cewa: “Na kuma sami kwarin gwiwa da cewa IGP mai barin gado ya kafa tushe mai kyau kuma ya kafa al’adar kwararru a rundunar.
“Wadannan za su kara min kwarin gwiwa a matsayina na sabon IGP mai rikon kwarya, don karfafa dabarunmu da samar da abin da ake bukata na shugabanci da zai sauya labaran dangane da dabarun gudanar da ayyukanmu game da barazanar da tsaro ke fuskanta a yanzu”.
Muna rokon Allah ya yi riko da hannun IGP Usman Baba Alkali wajan kawo zaman lafiya a cikin kasar mu Nijeriya.