Kwamitin majalisar wakilai kan harkokin kiwon lafiya ya yi barazanar bada izinin kamo shugaban hukumar dake kula da likitocin ƙasar nan (MDCN), Tajudeen Sanusi, matuƙar bai bayyana a gabansu ba gobe Jumu’a.
An gayyaci Sanunsi da ya bayyana a gaban kwamitin domin ya amsa wasu tambayoyi akan yajin aikin da ƙungiyar likitoci (NARD) ke yi.
Sai dai bisa dole yan majalisar wakilan dake cikin kwamitin suka ɗage taron bayan sun sami masaniyar cewa Sanusi na can ya haƙarci kotun hukumarsa.
Kotun dai ita ce wajen da ake yin hukunci a hukumar MDCN kuma tana da matsayin babbar kotu, tana hukunci ne akan likitoci idan bukatar hakan ta taso.
Shugaban kwamitin, Hon. Tanko Sununu ya ce Sanusi bai girmama gayyatar mu ba wacce take ta gaggawa amma yaje can ya halarci abinda ransa ke so.
Dan majalisar yace “Mun aika da gayyatar mu ga dukkan masu ruwa da tsaki da su halarci wannan taron, amma sai aka yi rashin sa’a shi yaƙi zuwa.”
“Saboda shine ginshiƙin taron, dole tasa muka ɗage taron daga yau, muka kira shi da ya bayyana a gabanmu kafin karfe 9:00 na safiyar gobe Jumu’a.”
“Idan kuma yaki zuwa a wannan lokacin da muka bashi to zamu yi amfani da ƙarfin majalisar ƙasar nan mu ɗauki matakin doka akansa, wanda ya haɗa da bada izinin kamo shi duk inda yake.
Sanunu ya kara da cewa ba zai yuwu mu zauna mu zuba ido muna ganin mutane na shan wahala saboda yajin aikin likitocin ba, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Hakanan muna kira ga likitocin da suka tsunduma yajin aiki da su dubi Allah su saka tausayi a zuƙatansu. Kowa yasan cewa suna da gaskiya a duk buƙatunsu, amma akwai wasu hanyoyi na daban da zasu iya cimma bukatunsu.
Sai dai har yanzun Shugaban MDCN ɗin bai maida martani kan gayyatar da yan majalisun suka sake yi masa ba ranar Juma’a