Shugaban hukumar karɓar korafin jama’a da yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya sake tabbatar da cewa a shirye yake ya ba da shawarar dakatar da Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, idan an samu yana da hannu a sayar da fili na gidan mai martaba ba bisa ka’ida ba.
A wata hira da ya yi da manema labarai, Muhuyi Magaji ya bayyana cewa hukumarsa ta gano cewa wasu jami’an fadar sun sayar da filin ba bisa ka’ida ba a Dorayi, a kan kuɗi Naira Milyan 200,000,000.
Amma duk da haka ya bayyana cewa, sun gayyaci jami’ai uku na fada don su ba da bayanansu, saboda kamfanin da ya sayi filin ya ambaci sunayensu.
Jami’an sun hada da Sarki Waziri Dan Rimi, Isa Pilot da Awaisu Abbas Sunusi, wanda shi ne sakataren fadar.
Idan za a tuna, a kwanakin baya ne Muhuyi ya fara binciken mai martaba Sarkin Kano na yanzu, Alh Aminu Ado Bayero, kan batun sayar da filaye a Gandun Sarki, Dorayi Karama, da ke karamar Hukumar Gwale ta jihar.
Ya kuke Ganin Wannan Binkice na Muhuyi?