Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun kama wani matashi mai shekaru 27, Abubakar Musa da ya yi garkuwa da kawunsa Kuma ya karbi kudin fansa har Naira miliyan daya.

Kakakin rundunar Abdullahi Kiyawa ya sanar da haka a wani bidiyo da ya aika wa manema labarai a garin Kano.

A bidiyon Kiyawa ya ce an kama Musa da manyan bindigogi biyu Ak 47 wanda yake amfani da su wajen aikata miyagun ayyuka.

Ya ce binciken da suka gudanar ya bayyana musu cewa Musa na daya daga cikin masu garkuwa da mutane da suka addabi mutane a Birnin Gwari, Kaduna, Kano da sauran jihohin Arewa.

Kiyawa ya ce a Jihar Kano Musa mazaunin kauyen Rurum ne dake karamar hukumar Tudun-Wada kuma ya shiga harkar yin garkuwa da mutane ne bayan an yi garkuwa da ‘yarsa da matarsa.

“Tun a baya dama ni barawon shannu ne a lokacin da na fara harkar yin garkuwa da mutane shekaru shida da suka wuce mutum uku kadai na taba yin garkuwa da su.

“Na yi garkuwa da kawuna Alhaji Haruna sannan na yi garkuwa da wasu ‘yan uwana biyu Bappan Jauro da Medi saboda sun yi garkuwa da kanwa ta Hafsat.

“Na aro wadannan bindigogi daga wajen wani Muhammadu Bakanoma a jihar Zamfara domin na tunkari wani Malam da nake zarginsa da yin garkuwa da matata da ‘yata.

Kiyawa ya ce Musa na hannun ‘yan sanda inda za a ci gaba da gudanar da bincike a kansa.

Yin garkuwa da mutane domin karban kudin fansa ya zama ruwan dare a yankin Arewacin Najeriya.

Banda sace matafiya da mahara ke yi a manyan titunan kasar nan abin ya koma har makarantu suke afkawa su tattara yara su yi awon gaba da su.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *