Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Bayan an yi juyin mulki na 1967, duk lokacin da Janar Murtala Mohammed ya hadu da Dan Masanin Kano Dr. Yusuf Maitama Sule sai ya ringa yi masa irin wasan nan na malami da dalibinsa.

Ya kan ce masa, “mun dai kori ‘yan siyasa sai a je kuma a nemi sana’a”. Shi kuwa Dan Masani sai ya maida masa da cewa, “ai ka san Akuya ko bata haihuwa ta fi kare”. A haka suke raha duk lokacin da suka hadu.

Rannan sai Janar Murtala ya zama shugaban kasa, ya kuwa tashi haikan akan yaki da zalunci da rashawa da ya addabi Najeriya, kusan komai gaskiyar ka kana shakkar ace Janar Murtala na neman ka. Kwatsam rannan sai ya aiko a gayawa Dan Masani cewa yana neman sa a Dodan Barracks (fadar gwamnati da ke Lagos kafin a dawo Abuja).

Dan Masanin Kano ya kwana yana jan Lahaula, saboda bai san neman da Murtala yake yi masa ba. Da safe ya hau jirgi, ya nufi Lagos, ya sauka a Airport, sai ya nufi Dodan Barracks, yana zuwa aka sanar da shugaban kasa, sai shi kuma yace a shigo da shi ofishin sa.

Da aka kai shi gaban Janar Murtala, suka gaisa sai Janar yayi masa barkwancin da ya saba yi in sun hadu cewar:

“Mun dai kore ku ‘yan siyasa, sai a je a nemi sana’a”. Sai Dan Masani yayi shiru, Janar Murtala yace, “Allah Ya gafarta ya kayi shiru?”

Sai Dan Masani yace:

“Ai kai a Karnukan ma Karen As’habul Khafi ne, wanda aka ce za’a shiga Aljanna da shi”.

Nan fa take Janar Murtala ya fashe da dariya ya ce masa, “To dama ina son in baka shugaban Hukumar Koken Ma’aikata ne (Public Complaints Commission).

Allah Ya jikan Janar Murtala, Ya jikan Dan Masani, Ya sanya Aljanna ta zama makomarsu gaba daya. Amin

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *