Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Dr Obadiah Mailafia, ya ce Najeriya karkashin jagorancin Janar Sani Abacha ta fi tsaro fiye da lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari.
Dakta Mailafia ya yi ikirarin cewa kasar Najeriya a zamanin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Sani Abacha, ta fi tsaro fiye da wannan gwamnatin.
“Wannan kwata-kwata ba a taɓa yin irinsa ba. Wannan shi ne mafi munin lokaci da aka taba gani a tarihin Najeriya. Ba kwa iya kwatantawa da lokacin Abacha; Lokacin Abacha ya kasance zamanin zinare idan aka kwatanta shi da abin da ke faruwa yanzu.”
“Shin kuna ganin inda Abacha ne zai jure duk wadannan kashe-kashe da lalata abubuwa ko’ina,” in ji Dr Mailafia.