Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

An samu karin mutum miliyan 7.9 da suka mallaki wayoyin hannu a arewacin Nijeriya kawai kamar yadda rahoton Hukumar Kididdiga ta kasa ya nuna.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani sabon rahoto da ta fitar, inda ta ce yayin da mutum miliyan 51.52 ne suka mallaki wayar hannu a 2019, masu wayar sun karu zuwa mutum miliyan 59.48 a 2020 wato cikin shekara daya kawai.

Wanda hakan a cewar hukumar ke nufin an samu karin kashi 15.5% na mutanen da suka mallaki wayar hannu a 2020.

Kididdigar ya nuna cewa a Arewa maso Yamma kawai, an samu karuwa daga mutum miliyan 10.99 a rubu’in karshe na 2019 zuwa mutum miliyan 12.67 zuwa karshen shekarar a Kano.

Inda kuma a Kaduna wacce take na biyu aka samu mutum miliyan 8.71 suka mallaki wayar hannu, wanda hakan ke nuni da cewa an samu kari daga 582,640 zuwa miliyan 8.12 daga 2019 zuwa 2020

Idan aka koma arewa ta tsakiya kuwa, mutanen da suka mallaki wayar sun karu daga miliyan 6.58 a farkon 2020 zuwa miliyan 37.07 a rubu’in karshe na 2020. Wanda hakan ke nufin yankin ya mallaki kashi 18.1 na masu wayar hannu a Naijeriya baki daya.

Babban birnin Tarayya Abuja ne kan gaba a yawan mutanen da suka mallaki wayoyin hannu inda ake da mutum miliyan 9.01, wato karin mutum miliyan 3.3 idan aka kwatanta da mutum miliyan 5.7 da ke da wayar a 2019.

Jihar Neja ce take biye da ita da mutum miliyan 6.53 idan aka kwatanta da mutum miliyan 6.22 a baya.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *