Kwanaki kadan bayan rasuwar dan majalisar tarayya, Haruna Maitala, wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Lere ta tarayya a jihar Kaduna, Suleiman Aliyu, ya rasu yana da shekaru 53 a duniya.
Aliyu ya rasu a yau Talata da rana a asibitin koyarwa na Barau Dikko dake jihar Kaduna bayan gajeriyar rashin lafiya.
Cikin kwanakin nan ne dan majalisar yayi nasara a kotun daukaka kara inda aka jaddada shi a matsayin dan takara kuma wanda yayi nasara a zaben ranar 23 ga watan Fabrairun 2019 na mazabar Lere a tarayya.