Duk da yunkurin juyin mulkin da akasoyi a kasar Nijar Wanda baa samu nasara ba , an rantsar da Mohamed Bazoum, a matsayin sabon shugaban kasar jamhuriyyar Nijar.
An rantsar da shi ne a ranar Juma’a, 2 ga watan Afrilu, 2021.
Gabanin yanzu, Bazoum ya kasance Ministan harkokin cikin gida kuma babban na hannun daman shugaba mai barin gado, Mahamadou Issoufou.
Wannan shine karo na farko tun lokacin da janhurriyar Nija ta samu yanci daga mulkin mallakar kasar Faransa da wani shugaban demokradiyya zai mika mulki ga wani shugaba ta hanyar zabe.
Sau hudu ana juyin mulki a tarihin kasar Nijar, mafi kusa wanda ya faru Febrairun 2010 inda aka tunbuke shugaba a lokacin, Mamadou Tandja.
Amma cikin awanni 48 da suka gabata, kasar ta fuskanci barazana da dama daga wasu yan yunkurin tada zaune tsaye.
Daga cikin wadanda suka halarci taron rantsar da Bazoum akwai gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje; Attajiri Alhaji Aliko Dangote, da Sarkin Kano mai murabus, Muhammadu Sanusi II