A yayin da ake ta kokarin shawl kan halin da mutane suka tsinci Kansu a jihar kano sakamakon ci ko shan gurbatattun abin sha Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta ce bakon rashin lafiya da ya bullo a Kano ya samo asali ne daga guban abinci.
Mojisola Adeyeye, darakta-janar na NAFDAC, ta tabbatar da hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.
Jaridar The Cable ta ruwaito yadda barkewar wani sabon cuta da ya haifar da mutuwar mutane biyu tare da kwantar da wasu 183 a asibiti a jihar.
Ya zuwa lokacin rahoton, ana zargin musabbabin cutar guba ne ta abinci.
Shugaban riko na hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan a hirar da ya yi da BBC.
Baffa ya ce bincike ya nuna cewa wadannan sinadaran da ake hada kayan shaye-shaye da su da yawansu lokacin ingancinsu ya kare, don haka babu mamaki dan an ce suna cutar da masu amfani da su.