A karon farko.a tarihi kungiyoyin Giodano fc karkashin Jagorancin Jamilu Wada Aliyu da Clever Warriors Karkashin Jagorancin. Najb Kurawa ya suyi fito na fito da neman gurbin zama na daya a gasar ajin matasa rukuni na daya a a shiyyar Jos,,
Kungiyar Giodano fc ce ke kan gaba a gasar da maki 10 bayan datayi nasara a wasanni 3 da kunnen Doki daya a wasanni 4 data buga kuma kungiya daya tilo da batayi rashin nasara ba tun fara gasar, a yayin da kungiyar Clever Warrious da suka fito daga gari daya ke biye mata da maki 9 a wasanni 4 data buga inda tayi tayi nasara 3 tare da rashin nasara a wasa 1
Daga dukkan alamun jihar kano ka iya samun gurbi duba da yadda kungiyoyin biyu ke taka rawar gani a gasar ta bana, kungiyar Giodano wacce ta dawo rukunin matasa bayan shafe shekaru biyu tana fafatawa a gasar ajin kwararru NNL ba tare da gajiyawaba na son ganin ta koma gidanta na ainihi duba da kalaman shugaban kungiyar Jamilu Wada wanda yace lokacine yayi da kungiyar zata koma wasan kwararru kuma a shirye muke mu. cigaba da bugawa duk da kalu balen kashe kudi da rukuni ke dashi inda Jamilu ya kara da cewa :
” Kowa yasan yadda na shirya Giodano shirine na tabbatar da anci gaba da bunkasa cigaban matasa a wannan harka ta kwallon kafa,duk da ba gwamnati banemu amma yadda muka samar da yanayi wanda yayi dai dai da zamani na gudanar da wasan kwallon kafa wanda kai shedane tsawon shekaru mukeyi ba gajiwa abin a yabane”
” Kuma mu burinmu in mun samu wannan dama bugawa zamuyi ba siyarwa zamuyi ba”
” A ciki muke kuma kowa yasani ko.lokacin da muka fadi ba muyi fushi ba cigaba mukayi har Allah ya kawomu wannan lokacin fatana shine Allah ya bamu sa’a kamar yadda yake bamu tunda muka fara ”
shi kuwa shugaban kungiyar Clever Warriors Najib Kurawa a tatraunawarsa da expressradiofm.com cewa yayi ” wannan shine karo na farko da muka shigo wannan gasa kuma muke samun nasara a ciki burina shine na sami.tikitin shiga rukunin kwararru da nima na dana yadda ake buga rukunin ”
” Kowa nason ace ya sami cigaba to muma haka mukeso ace a karon farko mun samu wannan damar duk da cewa akwai babban kalu bale a gabanmu amma ashirye muke dan tunkarar sa” inji Najib kurawa
Kungiyoyin Giodano fc da Clever Warriors na wakiltar jihar kano a wasan ajin matasa rukuni na daya kuma a litinin din zasu fafata wasan karshe a rukuni a shiyyar Jos dan samun wanda zai kai wasan karshe.