Duk da irin nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Giodano take samu a gasar wasannin ajin matasa na kasa da kungiyoyin suke fafatawa a garin jos inda kungiyar ke Jan ragamar gasar shugaban kungiyar Jamilu Wada ya gargadi yan wasan da masu horar da kungiyar da su kara zage dantse,
A tattaunawarsa da manema labarai jim kadan baya kammala wasa na 3 da kungiyar tayi kunnen doki bayan nasarori 2 da kungiyar tayi inda take jagorantar shiyyar da maki 7 a wasanni 3 da suka buga,
Jamilu wanda yace na gamsu da yadda yan wasana ke taka Leda da yadda masu horarwa da jagororin kungiyar ke aiki tukuru dan ganin an samu nasara a koda yaushe abinda kowa ke jin dadi,
Dangane gargadin da yake Jamilu Wada cewa yayi ” Giodano na daga cikin kungiyoyin da aka sawa ido a wannan gasar saboda wannan itace gasa ta farko tun bayan fadowar kungiyarmu daga rukunin kwararru saboda haka there’s too much espectation from us”
Jamilu ya kara da cewa muna bukatar samun nasara a kowane wasa daya rage mana dan shine zai bamu damar zama kan gaba, wanda hakanne zai sanya mu sami tikitin shiga rukunin da muka baro,
A dayake amsa tambaya kan damar da kungiyar ke da ita na samun komawa rukunin kwararru Jamilu Wada cewa Giodano nada dama amma muna bukatar sake zage dantse