Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Sojojin Najeriya sun ragargaji yan ta’addan Boko Haram a artabun da sukayi a karamar hukumar Marte ta jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar Jaridar PRNigeria, wannan artabu ya auku ne ranar Talata, 9 ga watan Maris, 2021.

Sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta’addan a farmakin da suka kai musu a garuruwan Hausari da Missene da Chikungudu da ke cikin ƙaramar hukumar Marte.

Rahoton ya kara da cewa yan ta’addan sun hallaka Sojoji biyu yayinda bakwai suka jigata.

Bayan haka, Sojojin sun samu nasarar kwace bindigogi kirar AK47 guda 27 da wasu bindigogin baro jiragen sama uku da kuma motocin yaki biyu.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *