Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya sanar da hakan a wata sanarwa da yayi a yammacin Talata, Daily Trust ta wallafa.
Ya ce da kanshi ya dauki kwanaki hudu a Abuja yana bayani ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran masu ruwa da tsaki a kan halin da tsaron jihar ke ciki.
“A cikin tattaunawar mu da shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran manyan kwamandojin tsaro a Abuja, an yanke shawarar cewa za a tura karin dakaru 6000 jihar domin karawa jami’an tsaron dake jihar karfi.
“Nan babu dadewa zasu iso domin fara aiwatar da ayyukansu, kuma muna mika godiya ga gwamnatin tarayya. Idan za ku iya tunawa, shugaban kasa ya umarci jami’an tsaro da su harbe duk wanda suka kama da makami ba bisa ka’ida ba.
“Shugaban kasa ya amince da wani wa’adi wanda yace ‘yan bindigan zasu iya miko makamansu domin zaman lafiya. Kamar yadda kuka sani mun samu nasarori a sasancinmu da ‘yan bindiga.
“Gwamnatin jihar ta yanke hukuncin daukan wadannan matakan: sarakunan gargajiya da mafarauta su kasance a garuruwan su domin sanya ido a kan masu shiga da fita yankin.
“Yawon fiye da mutane biyu a babur ya haramta, babu yawon babura a kungiyance a dukkan fadin jihar,” Matawalle yace.
Gwamna Matawalle ya kara da tabbatar da haramta ayyukan ‘yan sa kai a jihar tare da cewa duk wanda aka kama da bindiga zai sha mamaki.