Hukumar dake shirya jarabawar fita ɗaga sakandire (WAEC) tace ta soke jarabawar “Litrature-in-English” da ɗalibai masu zaman kansu sukayi.
Sai dai zuwa yanzun basu bayyana dalilin soke jarabawar ba kamar yadda jaridar Thenation ta wallafa.
Ɗaliban sunyi jarabawar ne a ranar 26 ga watan Fabrairu. Hukumar tace za’a sake yin jarabawar a ranar 10 ga watan maris.An fara jarabawar (WAEC) ɗin ne ta ɗalibai masu zaman kansu a ranar 15 ga watan fabrairu.
Bayan haka, WAEC ta fitar da sabbin matakan da za’a bi don yin rijistar jarabawar ga ɗaliban makarantun gwamnati.
Hukumar ta ce, kowacce makaranta sai ta biya N13,950 a ɗaya daga cikin bankunan da suka amince da su.