Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

 

Fafaroma Francis ya tattauna da jagoran musulmi mabiya Shia a Iraƙi, Ayatollah Ali al-Sistani, a wata muhimmiyar ganawa tsakanin mabiya addinai biyu.

Wata sanarwa daga ofishin jagoran na Iraƙi bayan taron ta ce ya faɗa wa Fafaroman cewa hikima da hankali dole ne su shafe yaƙin cacar baka, kuma Kiristoci, kamar dukkan ƴan Iraki su zauna lafiya.

Fafaroma ya kai wa jagoran na Shi’a a Iraƙi ziyarar mai matukar tasiri a garin Najaf, a rana ta biyu ta ziyararsa zuwa Iraki – ziyarar farko da wani Fafaroma ya taɓa kai wa a kasar.

An ɗuki shekaru biyu ana tsara ganawar tsakanin Fafaroma da jagoran na ƴan Shi’a a Iraƙi.

Kungiyoyin ƴan Shi’a masu dauke da makamai sun daɗe suna kai wa kiristocin Iraƙi tsiraru hari.

Fafaroma daga nan zai kai ziyara Awr, mahaifar Annabi Ibrahim – Annabi mai daraja a addinin Islama da Kiristanci da Yahudanci.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *