Gwamnan jihar Borno ya dira sansanin gudun hijira domin tantance na gaskiya da na karya
Gwamnan ya tabbatar da kame ‘yan gudun hijra na bogi sama da 600 dake wawashe abinci
Gwamnan kai ziyara sansanin ne da tsakar dare domin gane wa idonsa abubuwan da ke faruwa
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umaru Zulum ya yi wa wani sansanin ‘yan gudun hijira dirar ba-zata inda ya gano daruruwan ‘yan gudun hijira na bogi.
Sanarwar da gwamnatin Borno ta aike wa BBC ta ce daga cikin ‘yan gudun hijira 1,000 da ke cikin kundin jami’an agaji a yankin, 650 daga cikinsu na bogi ne
Sanarwar ta ce gwamnan ya kai ziyara ne a sansanin kwalejin Mohammed Goni MOGOCOLIS inda ake kula da mutanen karamar hukumar Abadam a arewacin Borno da rikici ya rabasu da gidajensu.
“Gwamna Zulum ya yi shigar ba-zata ne sansanin ‘yan gudun hijirar da tsakiyar dare tare da rufe sansanin domin tantance yawan ƴan gudun hijirar,” in ji sanarwar.
Gwamnan jihar Borno ya dira sansanin gudun hijira domin tantance na gaskiya da na karya
Zulum ya tabbatar da kame ‘yan gudun hijra na bogi sama da 600 dake wawashe abinci