Yayin da ake ta kokari daidaita tsakanin makiyaya da alummar yarabawan jihar oyo Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a ranar Laraba ya nanata cewa jihar ba za ta bayar da filaye kyauta don kiwo ba, yana mai cewa kiwo kasuwanci ne na kashin kai, Channels Tv ta ruwaito.
Gwamnan ya fadi hakan ne a cikin wasu sakonni da ya wallafa a shafin sa na Twitter yayin da yake karin bayani kan wani bayani da ya gabatar a baya game da shirin sauya fasalin kiwon dabbobi a yayin taron tsaro da aka gudanar a ranar Litinin.
“An ja hankalina zuwa ga batu game da aiwatar da Tsarin Canji na Kiwon Dabbobin Kasa yayin taron tsaro na hadin gwiwa, a jiya. Don guje wa shakku, lokacin da na ce za mu aiwatar da shirin, ba ina nufin aiwatar da tallata shirin bane,” in ji Makinde a shafinsa na Twitter.
“Zamu dauki bangarorin da suke da amfani ga jihar mu. Kamar yadda na sha fada a lokuta da dama, matsayinmu a Jihar Oyo shi ne, kiwon dabbobi kasuwanci ne na kashin kansa kuma ya kamata a gudanarahi
Rikici tsakanin manoma da makiyaya ya kasance batun da aka dade ana yi a Najeriya. Ana zargin makiyayan da galibi ke kaura daga yankin arewacin kasar zuwa kudanci don neman wajen kiwo ana zargin wasi da aikata laifuka irin su satar mutane, fyade, da sauransu.