Mai horar da Kungiyar kwallon
Kafa ta Chelsea, Thomas
Tuchel, ya bayyana cewa dan
wasa David Alaba, wanda
yake shirin barin kungiyar
Kwallon qafa ta Bayern
Munchen a karshen kakar
wasa ta bana zai iya buga
Kwallo mai kyau a Chelsea.
Tun bayan da aka ci gaba
da kungiyar da zai
bugawa wasa a kakar wasa
mai zuwa idan an kammala
wasannin bana xan wasa
David Alaba ya bayyana cewa
nan gaba kadan zai bayyana
Kungiyar da zai bugawa wasa
kafin a kammala kakar wasa
kenan ta bana.
A watan daya wuce ne David
Alaba ya tabbatar cewar zai
bar kungiyar kwallon qafa
ta Bayern Munich a qarshen
kakar wasa ta bana, bayan
da suka kasa kulla sabuwar
yarjejeniya a tsakaninsu
duk da cewa sun daxe suna
tattaunawa.
Mai tsaron bayan xan qasar
Austria ya koma kungiyar
ta Jamus a shekarar 2008,
ya kuma xauki lokaci suna
tattaunawa a tsakaninsu don
tsawaita zamansa a kungiyar
amma rashin kuxi da shekaru
yasa basu iya daidaitawa ba
kuma ya yanke shawarar
tafiya wata gasar.
Tun farko kunshin
yarjejeniyar da Alaba da
Bayern Munich suka qulla za
ta qare ne a qarshen kakar
wasa ta shekarar 2020 zuwa
2021, wato qarshen kakar
wasa ta bana kenan sai dai
zakarun duniyar sunyi masa
tayi amma bai gamsar da
xan wasan ba inda rahotanni
suna tabbatar da cewa yana
son buga wasa a wata gasar
ne savanin kasar Jamus.
Alaba, mai shekara 28 a
duniya, ya ci kwallaye 33
a wasanni 415 da ya yi wa
Bayern Munchen, sannan ya
kuma lashe kofin zakarun
turai na Champions League a
qungiyar a shekarun 2013 da
kuma 2020 data gabata.
An daxe ana alkanta Alaba
da cewar zai koma buga gasar
Premier League ta qasar
Ingila, wasu rahotannin na
cewar Real Madrid ce za ta
Sauke shi domin ya dunga
tsare mata baya daga tsakiya
ko kuma daga gefe.
Contact Information
Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York
We Are Available 24/ 7. Call Now.
- 2 October, 2023
Share: