Sabanin yadda wasu kafafen yada labarai na yanar gizo suka dinga yada labarin sakin daliban Makarantar Sakandiren ‘Yan Mata, ta Jangebe dake jihar zamfara da kuma wasu majiyoyi marasa tushe da kuma kishin-kishin da jaridar Punch a jihar Zamfara ta bada.
Hakan Ya fitone cikin wata takarda da aka rabata ga manema labarai, Wanda ke dauke da sa hannun Darattan yada labarai na gwamnatin jihar zamfara, Ya kara da cewa gwamna Bello Mohammed Matawallen Maradun da mataimakansa tun ranar Jumma’a lokacin da ‘yan bindiga suka sace’ yan matan ba su huta ba.
Ya Kara da cewa suna aiki ba dare ba rana don ganin an sami nasarar kubutar da wadanda aka sace , Ya ce gwamnati batayi farin ciki da cewa wani wanda bai san da hakan ba ,Kuma bashida cikakken bayani game da lamarin , zai yi kokarin kara cutar da iyayen wadanda abin ya shafa.
Gwamnan Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba, Gwamnatin jihar za ta zo da sanarwa da zarar an sako ‘yan matan,