Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya Rubuta a shafinsa na Facebook Yana Mai Cewa Bamu yiwa kanmu adalci ba a matsayin mu na ‘yan Najeriya dake son ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali ya samu a kasar nan, muddin muka yi shuru game da abubuwa marasa dadi dake ci gaba da faruwa a sassa da dama.
Abin tashin hankali ne mutuka, yadda ‘yan ta’adda ke ci gaba da sanya razani da fargaba a zukatan ‘yan Najeriya, wanda a yanzu wanda ke kan hanya ko cikin gida ko makaranta ba shi da tabbacin tsaro a inda yake.
Muna tsaka da fargaba da alhinin satar yara ‘yan makaranta a jihar Niger, wanda ake kokarin kubutarwa, sai gashi kuma mun wayi gari da samun labarin sace wasu daliban mata har guda 300 a makarantar sakandare dake karamar hukumar Mafara a jihar Zamfara.
Lokaci ya yi da zamu kawar da batun siyasa ko dora laifi kan wani, mu tunkari wannan kalubale dake neman hallaka mu muna cikin gidajen mu.
Wannan al’amarin dake faruwa babbar barazana ce ga bangaren ilmi a Najeriya, domin ana jefa fargaba a tsakanin iyayen yara, wannan ba batu ne na siyasa ba, ba batu ne na bangaranci ba, a’a batu ne na makomar ilimin kasa da tsaron al’ummar ta.
Ina amfani da wannan dama wajen addu’ar Allah Ya kubutar mana da wadannan yara da sauran wadanda ke hannun ‘yan ta’adda cikin koshin lafiya.
Ina addu’ar samun kwarin gwiwa da nasara ga jami’an tsaron mu, kada wannan ya sanya gwiwar ku ta yi sanyi, sannan ina kira ga al’umma su ci gaba da sanya idanu da kai rahoton duk wani abu da basu amince da shi ba ga jami’an tsaro.