Gwamnatin jihar Kano a ranar Asabar ta bada umurnin kulle wasu makarantun gaba da sakandare dake iyaka da wasu jihohin Arewa, Vanguard ta ruwaito.
Wannan ya biyo bayan garkuwa da dalibai mata 317 da aka yi a makarantar sakandaren GGSS Jangebe, karamar hukumar Talata Mafara a daren Juma’a.
Kwamishanar ilmin manyan makarantu, Dr Mariya Mahmoud Bunkure, ta ce daliban makarantun kwaleji hudu da aka bada umurnin rufewa su tattara kayansu su koma gida.
Dr Bunkure ya ce za’a sanar da dalibai lokacin da za’a sake bude makarantun.
Makarantun da za’a kulle sune:
1. Rabiu Musa Kwankwaso college of Advanced and Remedial Studies, Tudun Wada,
2. Makarantan koyar da ilmin yanayi, Gwarzo
3. Makarantar fasaha da cigaban kere-kere ( SORTED), Rano
4. ABCOAD, Dambatta.