Babban Limamin Masallacin Haramin Makkah mai alfarma da ke Makkah Sheikh Abdulrahman Sudais ya bayyana cewa tunda aka soma annobar cutar Coronavirus a duniya, duk da an samu masu dauke da cutar a kasar ta Sauriyya, amma har yau ba a samu mai dauke da cutar a Masallatan Makkah da Madina ba.
Sheikh Sudais ya bayyana haka yana mai farin ciki da godiya ga Allah kan haka. Sheikh Sudais ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da shafin Haramain Ash-Sharifain a ranar Laraba.