Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, ya ce nan ba da dadewa ba Najeriya za ta shawo kan matsalolin tsaro da take fuskanta
IBB ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 23 ga watan Fabrairu, a Minna, babban birnin jihar Neja
Tsohon shugaban kasar ya ce an sanar da shi cewa hukumomin tsaro suna aiki tukuru don kawo karshen ta’addanci a kasar
Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce za a iya magance barazanar tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu ta hanyar yin dogon shiri.
Channels TV ta ruwaito cewa a Babangida, a wata hira da aka yi da shi a ranar Talata, 23 ga Fabrairu, ya ce kasar za ta iya shawo kan matsalar tsaro idan wadanda ke kan mukamai suka yi shiri yadda ya kamata.
Legit.ng ta tattaro cewa ya ce kawar da barazanar da masu satar mutane, ‘yan fashi, da masu tayar da kayar baya ke yi yana bukatar babban shiri, ya kara da cewa ba shiri bane na wani dan gajeren lokaci.