Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wata mata da ke neman sayar da jaririnta mai wata hudu da haihuwa a kan Naira dubu arba’in ta shiga hannu.

‘Yan sanda sun kama matar ce a lokacin da take ci gaba na neman mai sayen dan nata don ta samu kudin kashewa.

Da take bayani kan matar da aka kama, kakakin ‘yan aandan a Jihar Ebonyi, DSP Loveth Odah ta ce duk da bayanan da Rundunar ta yi wa matar da aka kama a ranar Juma’a, tana nan a kan bakarta na cefanar da dan nata.

“Ta shaida mana cewa zaman kanta take yi ce kuma tana da jariri da yanzu haka yake kuka kuma da zarar ta bar nan za ta ci gaba da neman mai sayen shi.

“Mun yi kokarin yi mata magana ta duba matsayinta na uwa ta janye maganar amma ta ki gamsuwa da hakan.

“Har fada mana take cewa da zarar muka bar ta ta koma gida da jaririn jefar da shi za ta yi kuma ba za ta fadi wanda ya yi mata cikin ba duk rintsi,” inji ta.

Yayin tuhumar matar, ta kekashe kasa cewa ita ba ta da kudin da za ta iya daukar dawainiyar kula da jaririn nata.

“Ni ‘yar Najeriya ce, shekaruna 32 kuma zaman kaina nake yi, jaririn nan watansa hudu da haihuwa kuma dana ne,” kamar yadda ta bayyana

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *