Kwamitin kwararru na kula da COVID-19 na jihar Kano, ya bullo da wani shiri na kula dada gida don kai wa ga mutane a yankuna masu nisa, a wani bangare na kokarin dakile yaduwar cutar.
Wata sanarwa daga hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar wanda jami’in yada labaran ta Mista Maikudi Marafa ya sanya hannu, ta bayyana hakan ne a ranar Asabar.
Ya ce kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Aminu Tsanyawa, wanda ya kaddamar shirin a ranar Asabar, ya ce ya zama dole a takaita yaduwar cutar a karo na biyu.
Kwamishinan ya jaddada cewa an horas da ma’aikatan kiwon lafiya tare da basu babura da magunguna don isa da yankuna, da nufin bada kulawar gaggawa ta kiwon lafiya.