Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wata fito na fito da artabu da akayi tsakanin yan bindiga da jama’a a wani kunan bakin wake da jamaar sukayi dan kare kansu daga hare hare da yan bindiga suka addabesu Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da ‘yan bindiga suka kai wasu anguwanni dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.

A cewar Aruwan, ‘yan sanda suna nan suna bincike akan yadda wasu matasa suka yi arangama da ‘yan bindigan a anguwar.

Fusatattun matasa sun kashe wane matashi da ake zargin ya hada kai da ‘yan bindiga, The Cable ta ruwaito.

Aruwan ya ce ‘yan bindigan sun fara kai harn Unguwan Sha’awa, inda suka kashe wani Ubangida Dogo har cikin gidansa.

A cewarsa ‘yan bindigan sun kai wani harin Ungwan Galadima har suka kashe wani Bulus Gwamna. Sannan sun kai hari Unguwan Gamu suka kashe wani Daniel Danlami.

“Har yanzu jami’an tsaro suna cigaba da bincike akan wani wanda ake zargin ya hada kai da ‘yan bindiga yayin kai harin karamar hukumar Kajuru. Alamu sun nuna cewa sai da ‘yan bindigan suka hada kai da wasu matasan garin kafin su kai harin,” a cewarsa.

“Jami’an tsaro sun kara gano yadda suka kai wa wani da ake kira ‘Doctor’, dan kauyen Kujeni, wanda matasan Maro suka dauki fansa a kansa, ya bayyana hakan kafin mutuwarsa, inda yace akwai sa hannunsa a harin.

“Ya ambaci wani Fidelis Ali, dan Maro, a matsayin daya daga cikin wadanda suke hada kai da ‘yan ta’addan. Tuni ‘yan sanda suka kama Ali kuma yanzu haka yana hannunsu, ” yace.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *