A yayinda ake murnar sakin fasinjojin wata motar gwamnati da yan bindiga suka sace sai ga labarin sakin Dalibai da malaman kwallejin kimiyya na gwamnati da ke Kagara da yan bindiga suka sace sun shaki iskar yanci,
Sakatariyar watsa labarai na gwamnan jihar Niger, Mary Noel-Berje ta tabbatar da sakinsu inda ta ce suna hanyar zuwa Minna
Mary Noel-Berje ta ce inda sun isa Minna babban birnin jihar Niger, gwamnan jihar Abubakar Sani-Bello zai tarbe su
An sako mutane 42 da yan bindiga suka sace daga kwallejin kimiyya na gwamnati da ke Kagara a jihar Niger, The Nation ta ruwaito.
Wadanda aka sace sun hada da dalibai 27, ma’aikata 3 da kuma iyalan ma’aikatan su 12.
Majiyoyi sun ce wadanda aka sace din suna kan hanyarsu na komawa Minna a yanzu.
Hakanan, sakatariyar watsa labarai na gwamnan jihar Niger, Mary Noel-Berje ta tabbatarwa Premium Times cewa an sako su a daren yau Lahadi 21 ga watan Fabarairun 2021.