Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Jagoran darikar kwankwasiyya ta duniya Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bada gudunmuwan kayan abinci ga yan Arewan da rikicin Shasha a jihar Oyo ya shafa, rahoton DT.

Tsohon shugaban karamar hukumar Tarauni, Muktar Umar Yarima, ya jagorancin tawagar Kwankwasiyya zuwa Oyo ranar Juma’a domin gabatar da gudunmuwar ga shugabannin Hausawa dake jihar a madadin Sanatan.

Kayan abincin sun hada da buhun shinkafa 200, katon 200 na ruwan gora, da kuma lemun kwalta katon 200.

Yayin gabatar da kayan, Yarima yace, “Jagoranmu ya samu labarin cewa mutanen nan sun rasa muhallunsu kuma suna cikin halin kunci kuma suna bukatan taimako.”

“Shi yasa jagoranmu ya bada gudunmuwar wadannan kayan abincin domin raba musu.”

Yarima ya yi kira ga shuagbannin su taimakawa mutanen da suka rasa muhallansu.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *