Gwamna Nasir El-Rufai ya baiwa matasa dabarun da za su yi amfani dasu wurin fatattakar tsofaffi irinsa daga siyasa
A wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Juma’a, ya yi kira ga matasa, masana da shugabannin addini da su taru su baiwa kasa gudunmawa
El-Rufai yace zanga-zanga da tada zaune tsaye ba zai taba haifar da da mai ido ba har sai mutanen kirki sun bayyana kawunansu don taimakon kasa
Gwamna Nasir El-Rufai ya baiwa matasa shawarwari da dabarun da za su fatattaki tsofaffi irinsa daga siyasa.
A wata tattaunawa da ‘Radio Now’s Urgent Conversation’ dake jihar Legas suka yi dashi a ranar Juma’a, ya yi kira ga matasa, kwararru a fannoni daban-daban da kuma shugabannin addini da su hada kawunansu wurin ciyar da siyasa da kasar nan gaba.
El-Rufai ya ce zanga-zanga da tayar da hankula ba za su kai kowa ko ina ba har sai mutanen kirki sun taru sun mika kawunansu ga taimakon kasarsu ta gado, Daily Trust ta wallafa.