Tsohon ministan Wasanni da Matasa, Barista Solomon Dalung ya yi tanbihi kan tabarbarewar tsaro a Nigeria musamman satar dalibai
Da ya ke bayani kan satar daliban makarantar Kagara dake karamar hukumar Rafi ta Jihar Neja da ya faru a baya-bayan nan, ya ce akwai sakaci daga hukumomin tsaro sannan akwai siyasa
Tsohon ministan ya ce akwai wasu yan siyasan da kokarinsu shine muzanta Shugaba Muhammadu Buhari duba da cewa shine jama’a suka wa kalon zai iya dai-daita kasar
A yayin da alamuran tsaro a najeriya me kara tabarbarewa tsohon ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.
A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa