Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai adawa a najeriya ta yi kira da cewa a gaggauta sallamar Ministan Tsaro, Manjo janar Bashir Magashi mai ritaya daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba saboda rashin yin aikinsa kamsr yadda ya kamata Daily Trust ta ruwaito.
Jam’iyyar cikin sanarwar da sakataren watsa labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce ta bukacin hakan ne furucin da ya yi na cewa jama’ar Nigeria marasa makamai su kare kansu daga hare-haren yan bindiga da yan ta’adda.
A cewar sanarwar, “Jam’iyyar ta bayyana ministan a matsayin mai sakaci, wanda bai san aikinsa ba kuma tabbacin cewa gwamnatin Buhari ta yi wa bata gari saranda kuma bata da niyyar yakarsu.
“Bamu taba tunanin gwamnati za ta kira jama’an gari marasa makamai da yan bindiga da yan ta’adda ke kaiwa hari ‘ragwaye’ ba yayinda wadanda aka zaba su kare su suna zaune a ofisoshinsu a Abuja.”
Sanarwar ta PDP ta ce irin wannan yunkurin kauce sauke nauyi na gwamna alama ne da ke tabbartwa cewa Nigeria na neman zama kasar da ta gaza a karkashin gwamnatin Buhari tunda gwamnati ba za ta iya aikinta ba na maganin yan bindiga da masu tada kayan baya.