Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Ranar masoya ranace da masoya a ko ina ke kokarin bayyanawa junansu irin soyayyar da sukewa juna a wannan karon Wata matashiyar budurwa ce a kafar sada zumuntar zamani ta twitter mai amfani da suna @ButterBibi ta janyo cece-kuce bayan ta bayyana tsabar soyayyarta ga mawaki Don Jazzy.

A wasikar da budurwar ta rubuta, ta lissafo jerin nagartattun halayen mawakin da yasa take son shi.

Ta yi dogaro da karamcinsa, kyawunsa da kuma yadda yake mutunta jama’a a matsayin abubuwan da suka sa take kaunarsa.

Lamarin da ya bai wa kowa mamaki shine yadda ta dora ruwa da maganin ciwon kai a kan wasikar inda tace za ta sha su idan ya ki karbar tayin soyayyarta.

Ma’abota amfani da kafar sada zumuntar sun ce sun dauki salon budurwar kuma za su rubuta wasika ga wadanda suka hango suna kauna.

Wasu kuwa sun sha mamakin lamarin ganin cewa ba wata babba bace. Wasu cewa suka yi tsabar son abun duniya ce ta sa budurwar mika kokon bararta ga mawakin.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *