Wakili a majalisar tarayya mai wakilintar karamar hukumar birnin kano da kewaya Honourale Shaaban Ibrahim Sharada yace lokaci yayi da gwamnan kanu Dr Abfullahi Umar Ganduje zai daina haddasa rigingimu a jamiyyar APC,
A tattaunawarsa da yan jaridu a makarantar firamare ta salanta inda dan majalisar yaje dan sabunta rijistar jammiyyarsa amma bai tarar da kowa ba,ya zargi Gwamnan da cewa yana da masaniya kan kin kawo masu sabunta rajistar dan ayi masa bita da kulli tare da makarkashiya duk da cewa shine wakilin alummar birnin kanon a majalisar wakilai kuma dan jamiyyar APC,
Solacebase ta ruwaito cewa rahotanni sun nuna irin yadda dan gantaka tayi tsami tsakanin Shaaban da Gwamna Ganduje inda ko a baya bayannan aka samu takun saka kan zaben fidda gwani na dan takarar shugaban karamar hukumar birni inda wakilin yace anyi karfa karfa tare da rashin adalci wajen fidda gwanin,
Shaaban yayi kaurin suna wajen zargin gwamanati Ganduje da yanka makarantu sai da kadarorin gwamnati da yanka makabartu da samar da filaye,
Sharada wanda yayi suna wajen biyayya ga shugaba Muhammadu Buhari yace gwamnan kano Ganduje nada masaniyar zaizo dan sabunta rijistar shiya ya hana masu sabunta rijistar zama dan sabunta masa tasa rijistar abin da yace akwai wata manufa,