Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Saleh Alhassan, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Haure na kasa, ya ce kungiyar a shirye ta ke ta mayar da martani kan kashe mambobin ta da ake yi a fadin Nigeria.

A tattaunawar sa da jaridar The PUNCH, Alhassan ya yi ikirarin cewa da yawan makiyayan da ake kai masu farmaki da kashe su a fadin kasar, mutane ne da basu ji ba basu gani ba.

Ya ce kungiyar ba za ta lamunci cin kashi da barazanar da ake yi wa makiyaya na su fice daga shiyyar Kudu maso Yamma ba.

“Babu wani wanda ya ke da iko (na korar makiyaya). Idan ka ce za ka kori makiyaya, za mu bijirewa wannan umurnin naka. Mun jima muna rayuwa a mawuyacin hali. Idan har ba mu yi bore ba, to karshe za a kakkabe mu daga doron kasa.

Idan ka kashe makiyayi, kar ka je ka yi bacci, za mu sake ziyartar ka, kuma ba wai don mun tsani kabilar ka ba ne. Mutane suna kaiwa makiyaya farmaki, kuma a hanyoyi daban daban, makiyaya sun gano yadda za su rinƙa daukar fansa,” a cewar Alhassan.

Duk wadanda su ka tafi zuwa jamhuriyar Benin, yanzu suna dawowa gida. Duk wadanda ke cewa za su haramta bakin makiyaya shigowa Nigeria to basu ma san me suke yi ba, ko ba su karanci dokar ECOWAS ba, babu wanda ya isa ya kore su.

“Wannan ya sa matakin da gwamnan jihar Bauchi ya dauka shine dai dai. Ba ka da wani iko na korar wani mutum daga wani yanki na Nigeria.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *