Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya ce sama da 60% cikin 100% na masu zanga-zangar #EndSARS ba su san dalilin da ya sa suka shiga zanga-zangar ba, jaridar Punch ta tuwaito.

Zanga-zangar #EndSARS ta sake dawowa a Legas ranar Asabar mai taken #OccupyLekkiTollGate, tare da masu zanga-zanga sama da 30, ciki har da Debo Adebayo, wani dan wasan barkwanci da aka fi sani da Mista Macaroni, wanda jami’an tsaro suka kama.

Amma, an gurfanar da masu zanga-zangar a gaban kotun tafi-da-gidanka a Legas, kuma an bayar da belin su.

Magashi, wanda ya yi magana a ranar Asabar bayan da ya je sake rajistar jam’iyyar APC a Kano, ya yi zargin cewa wasu daga cikin masu zanga-zangar ‘yan iska ne da barayi

– Ministan tsaro na kasa ya bayyana cewa da yawan masu zanga-zangar #EndSARS barayi ne

– Ministan yace, duk da haka akwai wadanda mutanen kwarai ne kuma mutanen girki

– Ministan ya jaddada cewa gwamnati ba za ta bari wasu bata-gari su hargitsa kasar ba

Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya ce sama da 60% cikin 100% na masu zanga-zangar #EndSARS ba su san dalilin da ya sa suka shiga zanga-zangar ba, jaridar Punch ta tuwaito.

Zanga-zangar #EndSARS ta sake dawowa a Legas ranar Asabar mai taken #OccupyLekkiTollGate, tare da masu zanga-zanga sama da 30, ciki har da Debo Adebayo, wani dan wasan barkwanci da aka fi sani da Mista Macaroni, wanda jami’an tsaro suka kama.

Amma, an gurfanar da masu zanga-zangar a gaban kotun tafi-da-gidanka a Legas, kuma an bayar da belin su.

Magashi, wanda ya yi magana a ranar Asabar bayan da ya je sake rajistar jam’iyyar APC a Kano, ya yi zargin cewa wasu daga cikin masu zanga-zangar ‘yan iska ne da barayi.

KU KARANTA: ‘Yan majalisu na duba kudirin dakatar da ‘yan jaridun da basu da digiri daga aiki

Ya ce, “Akwai babban nauyi na gwamnati, kuma hakan shi ne ta kare kowane dan Najeriya, ko wanene shi. A koyaushe muna yin imanin cewa idan aka ba da hankali, babu wani wakilin gwamnati da zai zauna ya dunkule hannu ba tare da yin wani abu ba.

“Kun san dunbin taron #EndSARS. Fiye da 60% cikin 100% daga cikinsu mutane ne waɗanda ba su ma san dalilin da ya sa suke wurin ba.

“Sun zo ne kawai don su shiga. Wasu daga cikinsu ‘yan damfara ne; wasu suna can suna sata. Suna son yin duk abin da suke tunani. Akwai ainihin mutane (daga cikin masu zanga-zangar).”

Ministan ya kara da cewa gwamnati ba za ta kyale “wasu marasa kishin kasa” su hargitsa kasar ta kowane irin rufa-rufa ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *