Juma’ar nan 11 ga watan Fabrairun 2021 ne za a yi jana’izar dattijon kasa kuma gwamnan farar hula na farko a jihar Legas, Alhaji Lateef Jakande, The Punch ta ruwaito.
Sanarwar ta fito ne daga bakin kwamitin abokan tsohon gwamnan ya da riga mu gidan gaskiya a yau Alhamis.
Kazalika, daya daga cikin yayansa, Deji, ya tabbatar cewa za a yi jana’izar mahaifinsa a ranar Juma’a misalin karfe 4 na yamma.