Wata babban kotun majistare da ke jihar Katsina ta bukaci a adana mata wasu mutane uku a gidan gyaran hali da ke jihar.
Kamar yadda kotun ta bayyana, ana zargin Aminu Isiya, Lawal Kanjal da Iliya Adam da laifin kai wa ‘yan bindiga bayanan sirri,yadda jaridar The Punch ta ruwaito,
Dukkan mutanen ukun da aka tsare ‘yan karamar hukumar Kurfi ne kuma har sai zuwa ranar 13 ga watan Afirilun 2021 lokacin da zasu koma gaban kotu,
A ranar Alhamis ‘yan sanda sun bayyana yadda aka gurfanar da Isiya bayan kama shi da aka yi a kan zarginsa da ake yi.
Isiya da kan shi ya kira sunan Kanjal da Adam a matsayin wadanda suke taimaka masa wurin aika-aikar.
An gano cewa su ukun suna samarwa ‘yan bindiga bayanai wanda suke amfani da shi wurin garkuwa da mutane a yankin. Sune suka bada bayanin da aka yi amfani da shi wurin sace Fiddausi da Fauziya Sani.
An gano cewa an sace ‘yan matan biyu daga kauyen Daram da ke karamar hukumar Kurfi ta jihar.
An gano cewa ‘yan bindigan sun kai hari kauyen bayan mutum ukun sun bada bayanan sirri ga wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Saminu Kwano.
Tuni ‘yan sanda suka fara tuhumarsu da hada kai wurin aikata laifi, zama ‘yan kungiyar ‘yan ta’adda da kuma taimakawa garkuwa da mutane.
Sajan Lawal Bello ya sanar da kotu cewa wadannan laifukan sun ci karo da sashi na 59, 288, 46 da 243 na dokokin Penal Code na Katsina.
Bello ya sanar da kotun cewa ana cigaba da bincike a kan lamarin kuma ya bukaci a dage shari’ar zuwa nan gaba.
Hajiya Fadile Dikko, alkalin kotun ta karba wannan bukatar kuma ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Afirilun 2021