Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana bacin ransa kan takwaransa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, wanda ya daura masa laifin halin da Fulani makiyaya ke ciki, rahoton Daily Trust.
Yayin magana a ranar Alhamis, gwamna Bala ya tuhumi Ortom na tsananta rikicin manoma da makyaya ta irin maganganun da yake yi.
Amma mai magana da yawun Ortom, Terver Akase, a martaninsa, ya ce gwamna Ortom ya yi mamakin kalaman gwamna Bala saboda yana kira ga sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya da ya rantse zai kare.
Ya ce yawancin kalaman da Bala Mohammed yayi kawai yana kokarin kare Fulani Makiyaya ne.
Yace: “Gwamna Ortom ya na mamakin shin wani sashen dokokin kasa gwamnan Bauchi ya dogara da shi na goyon bayan Makiyaya masu yawo da manyan makamai.”
“Abin takaicin da ke damun gwamna (Ortom) shine wai ya za’ayi mutumin da aka baiwa hakkin kare jama’a ya rika kalaman batar da mutane.”
“Ya jaddada cewa akwai bukatan shugabanni su yi hattara wajen yin abubuwan da ka iya kai kasar nan ga halaka.”