Wani rahoto da jaridar The Cable ta fitar ya nuna cewa Legas ta kasance yankin Najeriya mafi soyuwa ga masu saka hannun jari yayin da take kan gaba a jerin jihohin da suka fi jawo hankulan masu saka jari a shekarar 2020.
Har ila yau bisa rahoton jihar Lagas din ta zarce sauran jihohin kasar ciki harda Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Rahotonin wanda ya ambaci Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) a matsayin tushensa, ya nuna cewa Legas, cibiyar kula da tattalin arzikin Najeriya, ta jawo dala biliyan 8.31 a hannun jari.
Wannan ya wakilci kaso 85.7 na jimillar jarin da ya shigo kasar nan a shekara ta 202
Kalli jerin jihohin a kasa:
1. Lagos – $ 8.31 biliyan
2. Abuja (FCT) – dala biliyan 1.27
3. Abia – $ 56.07 miliyan
4. Niger – $ 16.36 miliyan
5. Ogun – $ 13.39 miliyan
6. Anambra – $ 10.02 miliyan
7. Kaduna – $ 4.03 miliyan
8. Sakkwato – $ 2.50 miliyan
9. Kano – $ 2.38 miliyan
10. Akwa Ibom – $ 1.05 miliyan