Rahotanni na cewa Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da halaka mutane 18 a kauyen Kutemeshi da ke masarautar Kuyello a yankin karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ‘yan bindiga sun kai hari kauyen da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Asabar.
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa maharan sun shafe awanni uku suna cin karensu babu babbaka, ba tare da jami’an tsaro sun kawo agaji ba.
Abdulrahman Yusuf, kansilan da ke wakiltar mazabar Kuyello, ya tabbatar wa da Daily Trust kai harin tare da bayyana cewa an raunata mutane 15 yayin harin.
“An kashe mutane 18 yayin da wasu mutane 15 suka samu raunuka. Wadanda suka samu raunuka za’a mayar da su asibitin Kaduna domin a duba lafiyarsu. Yanzu haka shiri muke yi na binne gawarwakin mutanen da muka rasa,” a cewarsa.
A cewarsa, akwai nisan kilomita hudu a tsakanin kauyen Kutemeshi da garin Sabuwa da ke jihar Katsina.