Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce masu kokarin kafa kasar Biafra da Oduduwa ba su da bambanci da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gumi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Pidgin a ranar Asabar yayin da yake sharhi kan halin rashin tsaro a kasar.

Malamin ya ce zai zama rashin adalci a ce ‘yan Nijeriya suna son a raba kasar saboda ayyukan wasu “ bata gari” wadanda kawai ke ingiza mugayen akidu da bukatunsu.

Malamin ya yi ikirarin cewa yawancin ‘yan Najeriya suna son dunkulalliyar kasa inda zaman lafiya da daidaito ya yawaita.

Ya ce: “Yawancin lokaci na kan ba da misali da Janar Murtala Mohammed, tsohon shugaban kasa daga Kano wanda tawagar Buka Suka Dimka ta kashe.

“Ya auri mata bayarbiya. Don haka, ina kuke son ‘ya’yansa su tafi idan al’umma ta rarrabu?

“Shin za su kasance tare da Yarbawa ko kuma Hausawa a Arewa?

“Duba, mu manta da waɗannan samarin marasa amfani. Ba su da bambanci da wadannan makiyayan.

“Wadannan mutanen da ke neman kafa kasar Ododuwa, Biafra ko Arewa duk rukuni guda ne na mutanen da ke Boko Haram.

“Mafi yawan ‘yan Najeriya suna son zama tare da sunan Najeriya. Kuma idan suna cikin shakka, bari mu gudanar da zaben raba gardama.

“Dubi zabe misali, miliyoyin kuri’u daga dukkan jihohin, walau daga APC ko PDP.

“Wannan yana nufin ‘yan Nijeriya a shirye suke su kasance tare a dunkulewar Najeriya. Wannan zaben raba gardama ne wanda yake nuna cewa mutane a shirye suke.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *