Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

.

Gwamnatin Kano ta ware naira miliyan 245 don gudanar da auren mata da yawa a fadin jihar

Har ila yau ta amince da sakin naira miliyan 274.2 ga kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars

Kwamishinan labarai na jihar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar

Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da naira miliyan 245 don gudanar da auren mata da yawa a fadin jihar.

A shekarar 2019 ne gwamnatin jihar ta aurar da mutane 1,500 a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar.

An sanar da hakan ne a cikin wani jawabi dauke da sa hannun kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammed Garba zuwa ga manema labarai a ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairu.

Majalisar ta kuma amince da sakin naira miliyan 274.2 ga kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars domin tafiyar da harkokin kakar wasannin kwallon kafa ta 2020/2021 yadda ya kamata.

A cewar sanarwar, majalisar zartarwar ta jihar Kanon ta kuma amince da fitar da naira miliyan 29.3 domin aikin allurar rigakafi na shekarar 2020/2021 a tsakanin alumomin makiyaya.

An dakatar da shirin tsawon shekaru uku da suka gabata saboda hatsarin kiwon lafiya da asarar tattalin arziki da ke damun wasu al’ummomin jihar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan ya ci gaba da bayyana cewa majalisar ta amince da sama da naira biliyan 1 da miliyan 200 don kammala aikin gyaran titin Ahmadu Bello Way.

Sai kuma naira miliyan 212.9 da aka amince da shi don sake gina dakunan kwanan mata na Dangote a jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano da ke Wudil.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *