Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kame mabarata 500 kan laifin saba dokan hana barace-barace a kan titunan jihar.
Kwamishanar harkokin matan jihar, Dr Zahra’u Muhammad Umar,ce ta bayyana haka yayinda ake shirin mayar da mabaratan jihohinsu na asalia ranar juma’a kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Dr Zahra’u ta ce an damke mabaratan ne a cikin birnin Kano kuma yawancinsu mata ne da yara.
“Wadanda aka kama sun hada da mata, maza da Almajirai. Yaran ba sa zuwa makaranta kuma basu da wani abincin kirki da suke ci,” tace.
A cewarta, an yanke shawaran kama mabaratan ne domin kare rana gobensu da kuma zamar da Kano da Najeriya wuri mai kyau.
“Mun gano akwai halaye mara kyau cikin mabaratan. Za mu cigaba da damke su domin tsarkake titunanmu daga laifuka iri-iri,” ta bayyana.
Dr Zahra’au ta bayyana cewa wata tsohuwa mai shekaru 70 da aka kama cikin na rike da Sigari da ashana.
“Ire-iren wadannan tsohuwar na iya lalata yara da al’umma gaba daya. Barace-barace na illa ga rayukan yaranmu, musamman idan aka dauki Almajirai aiki a gida,” tace.