Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hadaddiyar Kungiyar Tuntuba ta Arewa, AUCF, ta bukaci gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun ya yi murabus daga kujerarsa saboda abinda ta kira gazawarsa wurin kiyaye rayyuka da dukiyoyin al’ummar da ke jiharsa.

Kungiyar ta kuma yi Allah wadai ta ayyukan Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho da ake zargi da lalata rugar fulani a jihar a farkon wannan makon, SaharaReporters ta ruwaito.

Wannan na cikin sanarwar ta kungiyar, AUCF, ta fitar ne a ranar Alhamis a Legas ta bakin shugabanta Alhaji Shuaibu Dansudu.

Kungiyar ta ce, “Gwamna Abiodun ne babban mai tsaro a jihar amma abin takaici ya gaza samar da tsaro a jiharsa, har sai da ya gayyaci wani daga jihar Oyo domin ya zo ya yi masa aikinsa.

“Don haka muna kira ga gwamnan ya yi murabus daga matsayinsa domin akwai alamun ba zai iya aikin ba. Idan bai yi murabus din ba, gwamnatin tarayya ta janye jami’an tsaron da ta ba shi.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *