Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tsohon gwamnan jihar kano kuma Sanata mai wakiltar kano ta kudu a majalisar dattijai Alhaji Kabiru Ibrahim Gaya ya bayyana cewa lokaci yayi daya kamata yankin Kudancin Najeriya ya samar da shugaban kasa na gaba a shekara ta 2023 don yin adalci.

A bayanin da yayin zantawasa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Abuja kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.

Yace Arewa ta samar da shugaban kasa na tsawon zango biyu wato shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda a cewarsa yayi kokari wajen ci gaban kasar.

Sanata Kabiru Gaya wanda ya nuna muradinsa na son ganin yankin kudu ya samar da shugaban kasa na gaba ya nanata cewa hakan shine adalci

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce shine abunda ya kamata ayi dan tabbatar da hadin kan kasar

Daganan sai ya yi kira ga yan siyasa da su mutunta tsarin mulkin karba-karba don ra’ayin kasar.

A cewar sanatan, shugaban kasa Buhari na iya bakin kokarinsa a kan kasar.

“Kan lamarin shugabancin kasa a 2023, zan marawa shugaban kasa daga yankin Kudancin kasar baya. Lokaci yayi da ya kamata mu samu shugaban kasa daga yankin kudu yayinda Mataimakin shugaban kasa zai fito daga arewa.

“Ina ganin ya kamata ayi adalci wajen juya shugabanci ta yadda mutane za su yi amanna da tsarin; daga arewa har kudu za su rungumi junansu. Akwai bukatar Najeriya ya zama kasa daya. Kasa daya mai hadin kai,” in ji shi.

Kan kira ga sauya fasalin lamura, Gaya ya bayyana cewa ya kamata Najeriya ta ci gaba da kasancewa a matsayin kasa daya yayinda take inganta hanyar tattara kudaden shigarta.

“Allah ya san abunda yafi shiyasa ya sa mu a waje guda kuma nayi imani akwai dalilin hakan.

“Amma idan kace kana so ka sauya fasalin lamuran kasar ta hanyar amfani da kudaden shiga, cewa kowace jiha ta ci gashin kanta ko yankunan kasar suyi ta kansu, Ina ganin wannan ne tunanin wasu yan Najeriya

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *